Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Benue ya yi Murabus

Hyacinth Aondona Dajoh Tsohon Kakakin Majalisar Benue

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Benue, Hyacinth Aondona Dajoh, ya ajiye mukaminsa.

Wannan lamari ya faru ne kwana biyu kacal bayan majalisar ta dakatar da wasu yan majalisa guda hudu na tsawon watanni uku bisa abin da takwarorinsu suka bayyana a matsayin shirin jefa zauren cikin rikici.

A cikin wasiƙar murabus ɗin da Dajoh ya rubuta da kansa, bai bayyana dalilin murabus ɗinsa ba, sai dai ya ce an yi hakan ne da kyakkyawan niyya.

A cewarsa:

“Ina rubuto wannan wasiƙar ne don in yi murabus daga mukamina na Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Benue daga yau, 24 ga Agusta, 2027.

An yi hakan ne da niyyar alheri da kuma don amfanin jihar. Ina godiya ga abokan aikina bisa damar da suka bani na kasancewa na farko cikin daidaito.

Zan ci gaba da jajircewa wajen gudanar da ayyuka na a matsayin ɗan majalisa da wakilin mazabar Gboko West.”

Rahoto ya nuna cewa an gabatar da wasiƙar a zaman gaggawa da majalisar ta yi da yammacin Lahadi, inda aka karɓa kuma aka amince da ita. A yayin zaman, aka zabi sabon Kakakin majalisar, Alfred Aondoaver Emberga, ɗan majalisar da ke wakiltar mazabar Makurdi North.

Sabon Kakakin na shirin rantsar da shi nan bada jimawa ba.

Cikakkun bayanai na nan gaba…