Zaben 2027: PDP Za ta Hukunta Mambobin da ke Marawa Tinubu Baya

Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya ce yana nazarin ayyukan kin bin doka da wasu mambobin jam’iyyar ke aikatawa, musamman wadanda ke goyon bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027 mai zuwa.

Sakataren Yada Labarai na kasa na jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba, ya bayyana cewa abin da ya fi damun jam’iyyar shi ne yadda wasu fitattun mambobi ke bayyana ra’ayoyinsu a kafafen yada labarai na cewa suna goyon bayan shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), lamarin da ya saba wa kundin tsarin mulkin PDP (wanda aka gyara a 2017).

Ya ce, “Akwai damuwa matuka kan yadda wasu mambobinmu ke ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu a fili, suna sukar jam’iyya da bayyana aniyar su ta yin aiki don ganin APC ta samu nasara a zaben shugaban kasa na 2027. Wannan abu yana barazana ga hadin kan jam’iyyar mu da kuma dorewarta.”

Ya jaddada cewa sashi na 10 (6) na kundin tsarin mulkin PDP ya bayyana cewa: “BA WANI MAMBI NA JAM’IYYA DA YA DACE YA HADA KAI DA SAURAN JAM’IYYU KO KUNGIYOYI DOMIN CUTAR DA JAM’IYYAR KO GWAMNATINTA DA AKA ZABA.”

Ologunagba ya kara da cewa irin wadannan ayyukan na cin amanar jam’iyya suna haifar da rarrabuwar kawuna, rashin jituwa da kuma barin jam’iyyar ta rasa mambobi masu karfi, wanda hakan na iya rage nasarar jam’iyyar a zabe idan ba a dauki mataki cikin gaggawa ba.

“Saboda haka, da la’akari da bukatar kare jam’iyyar da dorewar nasararta a siyasa, NWC na PDP, bisa tanadin s