Bikin Yancin Kai: Gwamnati Tarayya ta Bada Ranar Laraba Hutu
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, a matsayin hutu domin bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai. Ministan Harkokin Cikin Gida, Hon. Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, inda ya taya ‘yan Najeriya murna – duka waɗanda ke gida da kuma waɗanda ke ƙasashen waje…
