Hauhawar Farashi: Yobe da Ogun Sun Zama Kan Gaba da Tsadar Kayan Abinci
Jihohin Yobe da Ogun sun samu mafi girman hauhawar farashin abinci a Najeriya, duk da cewa hauhawar farashi gaba ɗaya a ƙasar ya ragu zuwa kashi 15.15 cikin 100, a cewar sabon rahoto daga Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS). Rahoton ya nuna cewa Yobe ta samu mafi girman hauhawar farashin abinci na shekara-shekara da kashi…
