Zazzabin Lassa: NCDC Ta Ɗaga Ƙararrawa Kan Ƙaruwar Cuta a Jihohi 18
Hukumar Kula da Cututtuka da Rigakafi ta Ƙasa (NCDC) ta nuna damuwa kan yadda cutar zazzabin Lassa ke ƙaruwa a jihohi 18 da ƙananan hukumomi 67 a faɗin Najeriya. Hukumar ta danganta ci gaba da yaɗuwar cutar da ƙarin mace-mace da gibin da ake da shi a matakin jihohi wajen aiwatar da matakan dakile ɓarkewar…
