Trends

Idris Umar

Harin ’Yan Bindiga: Kebbi Ta Buɗe Makarantar GGCSS Maga Bayan Watanni Biyu

Gwamnatin Jihar Kebbi ta sake buɗe Makarantar Gwamnati ta ’Yan Mata ta Sakandare (Government Girls’ Comprehensive Secondary School – GGCSS), Maga, bayan shafe watanni biyu da ’yan bindiga suka kai hari makarantar. Matakin ya biyo bayan harin da ’yan bindiga suka kai makarantar inda suka sace ɗalibai mata 24 tare da kashe Mataimakin Shugabar Makarantar….

Read More

Kasafin 2026: Gwamnatin Tarayya Ta Ware Naira Tiriliyan 1.38 Don Fansho da Garatuti

Kudirin Kasafin Kuɗin 2026 ya ware Naira tiriliyan 1.38 domin biyan fansho, garatuti da sauran haƙƙoƙin tsofaffin ma’aikata a fadin hukumomin Gwamnatin Tarayya, hukumomin tsaro, hukumomin gwamnati (parastatals) da jami’o’i. A ƙarƙashin wannan rabon kuɗi, Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya zai karɓi Naira biliyan 94.54 domin fanshon ma’aikatan farar hula, ciki har da garatuti, kuɗin…

Read More

Kasafin Kuɗin 2026: Gwamnatin Tarayya Ta Ware N1.764 B Don Sabbin Tallafin Karatu na BEA

Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 1.764 a cikin daftarin kasafin kuɗin shekarar 2026 domin tallafa wa sabbin ɗalibai 300 na Najeriya a ƙarƙashin shirin Tallafin Karatu na Yarjejeniyar Ilimi ta Ƙasashe Biyu (Bilateral Education Agreement – BEA). An jero wannan tanadi a ƙarƙashin Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, kuma zai rufe kuɗaɗen alawus-alawus, inshorar lafiya,…

Read More