IMPI Ta Yi Hasashen Ci Gaban Tattalin Arzikin da Kashi 5.5 a 2026
Ɗaya daga cikin fitattun ƙungiyoyin ba da shawarwari kan manufofi a Najeriya, wato Independent Media and Policy Initiative (IMPI), ta yi hasashen cewa tattalin arzikin ƙasar zai bunƙasa da kashi 5.5 cikin 100 a shekarar 2026, bisa sabon tsarin tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta runguma. A cikin wata sanarwar manufofi da…
