Miliyan 1.4 Sun Karɓi Tabarau Kyauta a Ƙarƙashin Shirin Gwamnati – Minista
Aƙalla ’yan Najeriya 1,444,581 sun karɓi tabarau na karatu kyauta a ƙarƙashin shirin Gwamnatin Tarayya mai suna Effective Spectacle Coverage Initiative Nigeria (Jigi Bola 2.0), cikin shekara guda ta fara aiwatarwa. Ministan Ƙaramar Ma’aikatar Kiwon Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, Dr. Iziaq Salako, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Fadar Gwamnati, Abuja, yayin…
