Biyan Basussukan Da Aka Karɓa Da Danyen Mai Ya Ci N8.36 Tiriliyon a 2025
A shekarar 2025, kusan kashi 14.66 cikin ɗari na jimillar man fetur ɗin da Najeriya ta hako ya tafi wajen biyan basussukan da aka karɓa da jinginar da danyen mai. Bayanai daga rahotannin kuɗi na NNPC Limited sun nuna cewa manyan yarjejeniyoyin bashi guda huɗu—Project Gazelle, Project Yield, Leopard da Eagle Export Funding—sun ɗaure kusan…
