Matatar Dangote Ta Fitar da Ton 456,000 Zuwa Kasashen Afirka
Matatar man fetur ta Dangote ta kara fadada tasirinta a yankin Afirka bayan ta fitar da kwale-kwalen mai guda 12 na kayayyakin mai da aka tace, wanda ya kai ton 456,000 (kimanin lita miliyan 608), zuwa kasashe biyar na Afirka. An sayar da kayayyakin ne bisa tsarin Free on Board (FOB) ta hannun ‘yan kasuwar…
