Matatar Dangote Ta Rage Farashin Mai Zuwa ₦1,200 Kan Lita
Matatar Dangote Petroleum Refinery ta sake rage farashin man fetur, inda ta saukar da farashin PMS (Premium Motor Spirit) daga ₦1,275 zuwa ₦1,200 kan kowace lita, wato ragin ₦75, kamar yadda majiyoyin masana’antu suka tabbatar a ranar Laraba. Wannan mataki na zuwa ne makonni kaɗan bayan matatar ta ƙara farashin zuwa kusan ₦1,275 kan lita,…
